Bassirou Faye: Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabon Shugaban Senegal Mai Jiran Gado

Publish date: 2024-04-24

Bassirou Diomaye Faye ya kafa tarihi bayan nasarar lashe a kasar Senegal a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi 24 ga watan Maris.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

An sanar da nasarar Faye bayan doke tsohon Fira Minista kuma ɗan takara a jam'iyya mai mulki, Amadou Ba.

Matashin mai shekaru 44 zai kasance shugaban kasar Senegal na biyar a ranar 2 ga watan Afrilu bayan rantsar da shi.

Shugaban kasar mai barin gado, Macky Sall da ɗan takara Ba sun taya Faye murnar lashe zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta jero muku abubuwa 6 game da Faye.

Kara karanta wannan

Tinubu zai halarci jana'izar sojojin da aka kashe a Delta? Fadar shugaban ƙasa ta magantu

1. Shekaru

An haifi Bassirou Diomaye Faye a ranar 25 ga watan Mayun 1980 a Ndiaganiao da ke yankin M’Bour a Thies da ke kasar, cewar France 24.

Hakan ya tabbatar da Faye a matsayin matashi mai shekaru 44 wanda ya kafa tarihin zama mai matsakaicin shekaru da ya samu wannan damar.

2. Karatu

Matashin ya kammala karatun digiri dinsa a shekarar 2000 inda kuma ya samu shaidar digiri na biyu bangaren sharia.

Kammala karatunsa ke da wuya ya tsunduma harkar kula da karbar haraji a ƙasar, cewar Lamonde.fr.

3. Iyali

Allah ya albarkaci Bassirou Faye da mata guda biyu masu suna Marie Khone wacce Kirista ce sai kuma da Absa Faye Musulma.

Har ila yau, Faye ya na da yara guda hudu maza uku da mace daya wanda ya haifa tare da Marie.

4. Aiki

Sabon shugaban kasar kafin tsunduma harkokin siyasa ya kasance mai kula da haraji kuma babban lauya ne.

Kara karanta wannan

Zaben Senegal: Dan shekara 44, Bassirou Faye, ya kafa tarihi a siyasar Afrika

Ya kammala karatunsa na digiri na biyu a bangaren sharia wanda ya ba shi damar kasancewa babban lauya, cewar rahoton Vanguard.

5. Gidan yari

Faye ya shafe watanni 11 a gidan gyaran hali kan wata wallafawa a shafin Facebook wanda hukumomi suke ganin ya saba doka.

Bassirou ya shaki iskar 'yanci kwanaki 10 kafin gudanar da zaben shugaban kasa wanda kuma ya yi nasara.

6. Siyasa

Shugaban masu adawa, Sanko ya ayyana Faye a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PASTEF a watan Nuwambar 2023.

Har ila yau, tsohon shugaban kasar, Abdoulaye Wade da jami'yyarsa ta PDS ta marawa Faye baya domin samun nasara, cewar Al Jazeera.

Faye ya kafa tarihi a siyasar Afirka

Kun ji cewa Ɗan siyasar Senegal mai shekaru 44, Bassirou Diomaye Faye ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a Nahiyar Afirka.

Faye ya yi nasara ne bayan doke ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mukin kasar, Amadou Ba.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHCw1KegsplfZoJ5gZRrbmaeka6ybrnUoaCmpZGjeqKu1JussJlda3qlrYyymGajkaKuta2MpKxmq5Gjtm6zwKacZpyRYsCirs6nZKygpZyuo63NZqqeppWcrq17